HOTUNA: Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron ECOWAS na karawa juna sani karo na biyu na kashen Afrika.


An gudanar da taron ne kan tsarin zamantakewa da neman mafita gameda juyin mulki a jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki.



Taron ya sami halartar shugabannin kasashen Guinea Bissau, Senegal, Cote 'd' Ivoire, Ghana, Benin, Sierra Leone, da Togo, yayin da Liberia da Gambia suka samu wakilcin ministocin su kar harkokin ƙasashen waje.


A yayin taron an jiyo shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu yana bayyana yadda za suyi da Nijar bayan babban taron su.


A cewar sa taron ECOWAS kan Nijar zai zama wani muhimmin lokacin sauyi a ƙoƙarin mu na tabbatar da ƙarfin iko da hadin kan Afrika ta yamma.


Idan baku manta ba a baya Tinibu ya bawa Sojojin da sukai juyin mulki a Nijar su mika mulki ko kungiyar tai anfani da karfi don farmakar su lamarin da ake ganin yaki yiwuwa duba da ƙarewar wa'adin.


Meye ra'ayin ku?


© AMINTACCIYA