Maryam booth jarumar mai shekaru 28 da aka haifa a garin kano a nigeria, kasantuwarta tun tana yarinya karama mahaifiyarta wato zainab booth take fitowa a finafinan hausa, hakan yasa itama tun tana yarinyar karama ake sanyata a finafinai har ta girma ta kai wannan matsayin da ake kallonta da shi a kannywood a yanzu. jaruma ta fito a finafinai da yawa na kudancin nigeria da kuma na arewacin nigeria wato kannywood. kamar su dijangal, suwaga, gani ga ka.



UMMI RAHAB


Jarumar mai tashe a wannan lokacin wacce aka haifa a garin kaduna ranar 7 ga watan april 2003 inda take da shekaru 19 yanzu da haifuwa, jarumi adam a zango shi ya fara sakata a wani film suna ummi a lokacin tana yarinya karama, daga baya tabar fitowa a finafinai sai bayan ta girma

film nashi da ya shirya mai suna fain wata shakallo. wanda har yanzu tana fitowa a wasu finafinan.


AMUDE BOOTH



Amude ya kasance kanine ga jaruma maryam booth kuma shima ya kasance 'da ne ga jaruma zainab booth mai rasuwa shima dai tun yana yaro karami ake ganisa yana fitowa a finafinai.

MARYAM MALIKA

Jarumar da ta koma harkar fim kwanan nan bayan mutuwar auren ta wato maryam malika, tayi suna ne da kuma samun wannan lakabi na malika da ake mata a sanadiyar wani fim da ta fito a ciki mai suna malika, jarumar bayan ta girma ta fara fitowa ne a wani film mai suna wasila 2010 kuma a shekarar 2010 ta fara fitowa a finafinai bayan ta girma kamar yadda ta bayyana. jarumar akwai wani film da aka ganta ta fito a ciki a lokacin tana yarinya karama tare da marigayiya Balaraba Muhammah da ya ha shekaru 20 wanda shi ya tabbatar da cewa..... tana yarinya karamar take fitowa a finafinai.